Kone zai yi jinyar rauni

Aroune Kone
Image caption Dan kwallon Ivory Coast zai yi fama da jinyar rauni

Ana fargabar dan kwallon Everton mai buga wasa a gaba Aroune Kone, zai yi jinya har karshen kakar wasan bana bayan da likitoci suka samu matsala a jijiyarsa ta mahadar gwiwa.

Rabon dan kwallon na Ivory Coast mai shekaru 29 da wasa tun 19 ga watan Oktoba lokacin da kungiyarsa ta samu nasara akan Hull da ci 2-1.

Kone ya shiga Everton daga Wigan kan kudi fan miliyan shida inda ya biyo bayan kocinsa Roberto Martinez.