A na tsoron haduwa da mu — Pellegrini

Manuell Pellegrini
Image caption Pellegrini ya bugi kirji za su iya doke kowacce kungiya

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya ce kungiyarsa za ta iya doke duk wata kungiya da ta rage a gasar kofin zakarun Turai, bayan da suka kai matakin sili biyu kwale a karon farko a gasar.

City dai ta kasa haye rukuni a kakar wasanni karo biyu a baya a gasar kofin zakarun Turai, ta kai wasan kungiyoyi 16 da zasu fafata kafin kammala wasanni biyu, bayan da ta casa CSKA Moscow da ci 5-2.

Da aka tambaye Pellegrini ko zasu iya lashe duk wata kungiyar da suka hadu da ita? sai ya ce yana fatan haka, kuma suma za a iya doke su.

Ya kara da ce wa "ina da tabbacin duk wata kungiya ba zata yi farincikin haduwa damu ba.