An dakatar da Riether wasanni uku

Sascha Riether
Image caption Dan kwallon ya amince da tuhumar da aka yi masa

An haramtawa Mai tsaron bayan Fulham Sascha Riether, buga wasanni uku, bayan da ya amince da tuhumar da hukumar kwallo kafa ta Ingila tayi masa ce wa ya yiwa dan kwallon Manchester United Adnan Januzaj keta.

Al'amarin ya faru ne a lokacin da ake daf da tashi a wasan da Fulham ta sha kashi da ci 3-1 a hannun United ranar 2 ga watan Nuwamba.

Sai dai, ko da yake alkalin wasa bai ga ketar ba, amma an dauka a faifan bidiyo.

Karkashin sababbin ka'idojin da hukumar ta wata tawaga ta alkalan wasa su uku ne suka kalli wasan suka kuma same shi da laifi.