" Ba tabbacin daukar kofin Arsenal"

Rooney
Image caption Arsenal sun taba yunkurowa amma muka lashe kofi

Dan kwallon Manchester United, Wayne Rooney, ya ce sai a watan Maris za a tabbatar da hakikancin cewa abokan karawarsu, Arsenal -- da za su fafata ranar Lahadi -- za su iya lashe kofin Premier.

Arsenal tana saman tebirin Premier da maki biyar bayan buga wasanni goma, kuma ta bai wa United tazarar maki takwas.

Rooney ya ce, ''Mun san lokacin da suka dare matsayi na biyu a teburin, sai da aka shiga watan Fabrairu da Maris aka daina jin duriyarsu".

Ya kara da ce wa "Yanzu suna kokari matuka, ya rage gare su su ci gaba da rike matsayinsu, mu kuma muna kokarin tarar da su''.