Shin mai yasa zaka zabi Yaya Toure?

Rahoto daga Ian Hughes na BBC Sports

Image caption Lokacin da Nigeria ta doke Ivory Coast

Ba wannan ce shekarar da Yaya Toure ya fi samun Kofuna ba, amma 2013 cike ta ke da nuna bajinta ta gudu, juriya, kwarewa, fasaha, kwallaye da kuma jagoranci daga dan wasan na kasar Ivory Coast.

Wadannan dabi’u sun fito da shi a matsayin cikakken dan wasan tsakiya kuma watakila wanda yafi kowa kwarewa wurin gudu daga raga zuwa raga. Zai yi wuya a iya tuno wani mutum da ya mamaye harkar kwallon kafa kamarsa.

Shi kadai ne dan Africa a jerin ‘yan wasa 23 da hukumar Fifa ta ware sunayensu a matsayin ‘yan takarar gwarzon kwallon kafa na duniya, don haka zai yi wuya a samu wanda zai musanta cewa shi ne dan kwallon kafar da yafi kowanne zarra a nahiyar a daidai wannan lokaci.

A yayin da shi da sauran ‘yan kungiyarsa ke takaicin nasarar da abokiyar adawarsu ta Manchester United ta yi akansu ta lashe Gasar Premier a farkon shekarar nan, Toure ya fara sabuwar kakar wasa cikin kwazo, da kuma cikakkiyar niyyar kwato kofin daga United.

Toure shi ne gwarzon dan wasa a karon da City ta casa United 4-1 cikin Satumba kuma tuni ya zura kwallaye bakwai a gasar – ciki har da wadansu bugun tazara guda huda da ke nuna kwarewarsa a matsayin kwararren mai buga tsayayyar kwallo cikin raga.

A bayan fage kuma, Toure na jagorantar yaki da wariyar launin fata a kwallon kafa bayan da ya fuskanci tsangwama da cin fuska a wasan Gasar Zakarun Turai da suka buga da CSKA Moscow ta Rasha cikin watan Oktoba – abin da ke nuna ya na da jan halin da ya yi daidai da jajircewarsa a filin kwallo.

Wannan mummunan lamarin zai iya kawo cikas ga wasu ‘yan wasan da ba su goge ba, amma Toure sai kara himma y ke kamar wanda ake wa zuga.

Bajintar da ya ke cigaba da nunawa a filin kwallo da dattakun da ya ke nunawa a bayan fagge ya sa Toure ya zama zabi na a gasar gwarzon dan kwallon Afrika ta BBC ta bana.