Arsenal ta casa Borussia Dortmund 1-0

Mesut Otzil da Aaron Ramsey na murnar cin kwallo
Image caption Mesut Otzil da Aaron Ramsey na murnar cin kwallo

Kwallon da Aaron Ramsey ya ci da ka ta bai wa Arsenal nasara kan Borussia Dortmund, abinda ya tabbatar da kungiyar a matsayin jagorar rukunin F a gasar cin kofin Zakarun Turai.

A minti na 62 ne Aaron Ramsey ya isar da kwallon da Mesut Ozil ya bugo masa.

Arsenal ce kungiyar Ingila ta farko da ta yi nasara kan Dortmund a gidanta, kuma wannan ce nasarar Arsenal ta 14 cikin wasanni 15 da ta yi a waje ba tare da an doke ta ba.

Sau daya tak aka cinye Dortmund a gida cikin wasanni 60 kuma ta lashe gaba daya wasanni takwas da ta yi a gida na cin kofin Zakarun Turai.

Wannan nasarar ta Arsenal daukar fansa ce kan cinyeta da Dortmund ta yi a gidanta makonni biyu da suka wuce, amma babu tabbacin hakan zai basu damar isa mataki na gaba a gasar Zakarun Turan.

Ko da Arsenal ta lallasa Marseille da ke kasan tebur a wasan da za su buga a filin Emirates ranar 26 ga Nuwamba, ba za ta samu damar shigewa matakin gaba ba har sai ta samo akalla maki guda a wasanta na rukuni na karshe da za ta kara da Napoli.