Tarihin dan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang

Image caption Pierre-Emerick Aubameyang a gasar Bundesliga

Tsohon dan wasan matasa a AC Milan, Pierre-Emerick Aubameyang ya shiga kwallon kafa gadan-gadan ne lokacin daya koma Saint-Etienne a 2011.

Zamansa a kungiyar ya kare ne a watan Yuli lokacin da ya koma Borussia Dortmund, wacce ta zo ta biyu a gasar Zakarun Turai inda ya maye gurbin Mario Gotze wanda ya koma Bayern Munich.

A zamansa da Les Verts ne Aubameyang ya daga kofinsa na farko bayanda kungiyar ta lashe kofin kwallon kafa na Faransa a 2013.

Bai zura kwallo a wasan cin kofin ba amma dai dan wasan ya ci kwallaye 19 a kakar wasannin, inda Zlatan Ibrahimovic na PSG kadai ya dara shi jefa kwallaye a raga, yayinda dan Gabon din kuma ya taimaka aka ci kwallaye takwas.

Wannan bajintar ce ta sa Dortmund ta sayi dan wasan tsawon shekaru biyar kan £11m.

Nan take kuwa ya samu nasara yayinda Dortmund ta dau fansar kayan da ta sha a London a gasar Zakarun Turai bayan da ta casa Bayern Munich 4-2 ta lashe gasar Supercup ta Jamus a farkon kakar wasan bana.

Aubameyang shi ne dan wasa na shida a tarihin Bundesliga da ya zura kwallaye uku a raga a wasansa na farko yayinda Dortmund ta ragargaji Augsburg 4-0.

Ruwan kwallayen ya cigaba da kwarare inda Aubameyang ya mike kafa ya zuba kwallaye bakwai cikin wasanni 11 da ya bugawa yaran Jurgen Klopp.

A yayinda kwallon kafa a matakin kungiya ke yiwa dan wasan mai shekaru 24 kyau, 2013 shekarar takaici she gare shi a wasan kasa da kasa.

Duk da haka dan wasan ya nuna kwarewarsa inda ya ci bugun fenariti har guda uku a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya wacce suka kara da Nijar a watan Yuni, sai dai wannan ce nasarar da kungiyar ta Panthers ta samu kadai, inda ta kara a matsayi na uku a rukuninta, abinda ya fitar da ita daga jerin masu neman zuwa Brazil a 2014.