Zaben gwarzon kwallon Afrika na BBC na 2013

Image caption Wani dan kwallo ne zai ciri tuta a Afrika?

An bayyana sunayen 'yan kwallo biyar wadanda a cikinsu za a zabi gwarzon dan kwallon Afrika na BBC a 2013.

A karo na biyar a jere, dan wasan Ivory Coast Yaya Toure ya kasance a cikin jerin, sannan kuma akwai 'yan Nigeria Victor Moses da John Mikel Obi, da dan Burkina Faso Jonathan Pitrioipa sai kuma Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon.

Masoya kwallon kafa a Afrika ne zasu kada kuri'a don zaben gwarzon, inda za a rufe kada kuri'a a ranar 25 ga watan Nuwamba.

Zaku iya zabe ta hanyar ziyartar wannan shafin ko kuma ta hanyar aika sako a wannan lambar wayar +44 7786 20 20 08:

Aika 1 don zaben Pierre-Emerick Aubameyang Aika 2 don zaben Victor Moses Aika 3 don zaben John Mikel Obi Aika 4 don zaben Jonathan Pitroipa ko ku aika 5 don zaben Yaya Toure

Kamfanonin wayoyin salula zasu caji kudin aika sako. Kuma sako daya tal za a karba daga kowacce lambar waya.

Don kada kuri'a latsa nan

A ranar Litinin, 2 ga watan Disamba da karfe 1735 agogon GMT a shirin BBC na Focus on Africa radio da kuma na Talabijin za a sanarda wanda ya lashe kyautar.

Image caption Waye zakara a Afrika?

'Yan jarida 44 daga kasashen Afrika ne suka zabi sunayen wadanan 'yan kwallo biyar, kuma daga cikinsu babu wanda ya taba samun kyautar.

Pierre-Emerick Aubameyang ya haskaka a kakar wasa ta 2012 zuwa 2013 inda ya zira kwallaye 19 a kungiyarsa ta Saint Etienne, kuma ya kasance dan wasa na biyu a jerin wadanda suka ci kwallaye a gasar Faransa. Sannan kuma ya taimakawa kulob din ya lashe gasar kofin Faransa.

Wannan bajinta ce tasa, kungiyar Borussia Dortmund ta Jamus ta siyeshi inda yaci kwallaye 7 cikin wasanni 11.

Pitroipa kuwa ya ciri tuta ne a gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika da aka buga a Afrika ta Kudu inda aka bashi kyautar dan wasan da yafi kowa nuna hazaka, sannan ya taimakawa Burkina Faso takai zuwa wasan karshe.

Dan wasan Rennes din ya ci gaba haskakawa kasarsa, inda ya zira kwallaye uku a wasannin share fagen neman cancantar buga gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil.

'Yan wasa biyu dake cikin jerin sune na tawagar Super Eagles da ta lashe gasar cin kofin Afrika a bana, wato Mikel da Moses wadanda duk sun taka rawa sosai a Nigeria.

Mikel ya lashe kofuna da dama tare da Chelsea ciki hadda gasar Europa a bana, kuma yaci kwallo daya a wasanni 185.

Moses kuwa yaci kwallaye da dama a Chelsea kafin ya koma a matsayin aro tare da Liverpool, inda ya zira kwallo a wasansa na farko a Liverpool a watan Satumba.

Sai kuma Yaya Toure na Ivory Coast wanda ya kasance zakara tsakanin 'yan wasa a gasar Premier ta Ingila.

Koda yake tawagarsa ta Manchester City ta kasa kare kofinta na gasar Premier , amma dai Toure ya nuna cewar shi babban dan wasa ne.