Chelsea ta lallasa Schalke 3-0

Kocin Chelsea Jose Mourinho
Image caption Kocin Chelsea Jose Mourinho

Sau biyu Samuel Eto'o yana zurawa Schalke kwallaye a nasarar da ta baiwa Chelsea zarra a rukunin E na gasar cin kofin Zakarun Turai.

Jamusawan ne suka fara yunkurin ci inda Julian Draxler da Adam Szalai suka samu dama amma suka barar.

Sai dai sakacinsu ne ya ba Chelsea damar zura kwallon farko lokacinda Samuel Eto'o ya karbe kwallon da gola Timo Hildebrand ya buga.

Bayan rabin lokaci, Drexler ya kara yunkurin jefa kwallo amma golan Chelsea ya rike ta. Daga bisani Willian ya korawa Eto'o kwallo ya kara guda sannan Demba Ba ya cike ta ukun.

Wannan nasarar ta karawa Chelsea tazarar maki uku a saman teburin rukunin kuma idan ta samu nasara ko canjaras a wasan da za ta buga da Basel, tabbas za ta samu kai wa mataki na gaba.