Tarihin Dan kwallon Nigeria John Mikel Obi

Image caption Mikel Obi na murnar kwallon da ya ci Fulham a gasar Premier ta Ingila

A tsawon shekaru bakwai da ya yi a Chelsea, John Mikel Obi, ya buga wasanni 187 tare da daga kofuna da dama da suka hada da kofin Premier, Kofin Zakarun Turai, da kuma Kofin FA har guda hudu.

Saura kiris ya zama dan wasan Manchester United, domin kuwa kungiyar mai wasa a Old Trafford ta yi zaton ta kulla yarjejeniyar dauko dan wasan daga Lyn Oslo ta Norway lokacin ya na da shekaru 18. Sai dai bayan da aka sha tata-burza, Chelsea ta yi nasarar daukar matashin a Yunin 2006.

Tun daga wannan lokacin, Mikel bai yi kasa a gwiwa ba inda ya kafa kansa a matsayin cikakken dan wasan Blues da Nigeria – inda ya bugawa kasarsa wasanni 51 kuma ya taimaka ta cin kofin kasashen nahiyar Africa a bana.

Dan wasan tsakiya gwanin kare baya tare da ladabi, sai a cikin watan Satumban bana ne Mikel ya jefa kwallonsa ta farko a rukunin Premier a wasansa na 185 ga kungiyar Chelsea inda su ka yi nasarar 2-0 akan Fulham.

Ana iya cewa kokarinsa ya fi bayyana ne a wasan karshe na cin kofin Zakarun Turai da suka buga da Bayern Munich, lokacin da Mikel ya nuna bajintar rike baya, ta yadda kungiyarsa ta yi kunnen doki 1-1 bayan arangamar minti 120 tare da Jamusawan. Chelsea ta yi nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda ta daga kofin.

Muhimmancin Mikel ga Chelsea ya kara tabbata lokacin da kungiyar ta kara tsawon kwantiraginsa da shekaru biyar a bara domin ya cigaba da zama a Stamford Bridge har 2017.