Shin mai yasa zaka zabi Jonathan Pitrioipa?

Rahoto daga Piers Edwards na BBC Sport

Image caption Jonathan Pitrioipa

Babu wani dan wasan Burkina Faso da ya taba kusatar zama gwarzon dan kwallon Africa na BBC amma Jonathan Pitrioipa ya cancanci wannan kyauta.

Daya daga cikin fitattun ‘yan wasan nahiyar, dan wasan na gefe na da dadin kallo, inda ya kan haskaka wasan da yake ciki, ta hanyar yanka, da gudu, da kuma gwanintar rike kwallo.

Bayan da ya haska a wasannin nahiyar Africa na baya, tauraruwarsa ta yi hasken da a wasan karshe na bana, aka bayyana shi a matsayin gwarzon dan wasa.

Yana da muhimmanci a dubi girman wannan nasara saboda Burkina Faso ta isa Afrika ne ba tare da nasara a wasa ko daya daga cikin 21 da suka buga a nahiyar Africa ba.

Wannan lamarin ya sauya daga nasarar da suka yi ta 4-0 kan Ethiopia, inda dan wasan gefen na Rennes ya taka rawa cikin jefa kwallaye uku, kafin ya daga bisani ya jefawa Togo kwallon da ta kai su matakin kusa da na karshe a karo na farko tun bayanda kasar ta karbi bakuncin gasar a 1998 lokacin Pitroipa mai shekaru 11 na cikin ‘yan kallo.

Daga nan kuma sai ga Burkina Faso a wasan karshe na gasar a karo na farko a tarihi. Duk da dai ba su kai labari ba a wasan da suka buga a Johannesburg, Pitroipa ya ce wannan wasan ya bashi kwarin gwiwar da take tafe da shi a wasan neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.

Ta karshe a rukuninta cikin watan Maris, nasarori hudun da ta samu a jere, (ciki har da kwallayen Pitroipa biyu) sun kai Burkina Faso – wacce bata taba kusan samun shiga gasar ba zuwa matakin cike gurbi, inda Stallions ke jan Algeria 3-2 gabannin wasansu na biyu a Algiers ranar 19 ga Nuwamba.

Pitroipa ne ya zura kwallon da ta kawo nasara a gasar, kuma shekarar da yafi kowacce zuba kwallaye a wasan kasarsa ta dace da shekarar da yafi kowacce zuba kwallo a kungiyarsa – manyan dalilai biyu ke nan da suka sa wannan dan wasan gefen ya cancanci kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na bana.