Shin mai yasa zaka zabi John Mikel Obi ?

Rahoto daga Oluwashina Okeleje na BBC Sport

Image caption Mikel Obi ya nuna cewar ruwa ba tsaran kwando bane

Bayan da ya daga kofi a 2013, wannan ce shekarar da John Mikel Obi ya tabbatar da kansa a matsayin daya daga cikin ‘yan wasa masu matukar daraja a nahiyar Africa.

Babu wani dan wasa a nahiyar da ya haskaka a shekarar kamar dan Najeriyar, wanda ya fara kakar wasannin cikin nasara kuma ya cigaba da kara daukaka.

Mikel ya kai kololuwa a kwallon kafa cikin sauri amma tare da fuskantar kalubale. Shekarun da ya kwashe a matsayin dan baya a Chelsea sun rage kaifin kai harinsa a wasannin Super Eagles.

Bajintar da ya yi wa Nigeria a gasar cin kofin kasashen Africa 2013 ta tunawa masoyansa irin gudunmawar da yake bayarwa a tsakiyar fili.

A gasar da aka gudanar a Africa ta kudu, yana cikin manyan ‘yan wasan kungiyar duk da shekarunsa 25 kacal kuma ya nuna kwazo a can cikin fili fiye da matsayin bayan da ya saba bugawa a kungiyarsa.

Mikel ya buga dukkanin wasannin a gasar da Nigeria ta yi lashe kofin bayan da Super Eagles ta doke Burkina Faso 1-0 a wasan karshe.

Ya kuma nuna amfaninsa a Chelsea da irin kwazon da ya yi a gasar cin kofin Europa 2013.

Kodayake zakarun Afrika Nigeria ba su yi wata rawar gani ba a gasar Confederations Cup, Mikel ya buga cikakkun wasanni ukun da kungiyarsa ta yi.

A matakin farko aka fitar da Nigeria daga gasar kuma ta jefa kwallo daya ne a wasan da Uruguay ta doke ta 2-1.

Baya ga zura kwallo daya tilo da Super Eagles ta jefa a gasar, Mikel ya yi rawar gani a karawar da Spain ta lallasa Nigeria 3-0.

A matakin kulob kuwa, Mikel ya jefa kwallonsa ta farko a Premier a wasan da Chelsea ta yi nasara kan Fulham 2-0 a Stamford Bridge cikin watan Satumba 2013.

Mikel na fatan zama dan Nigeria na biyu da ya lashe gasar gwarzon kwallon kafa na Afrika daga Nigeria. Dan Nigaeria daya ne tak, Jay Jay Okocha ya taba cin gasar inda ya lashe sau biyu a jere (2003 da 2004).

Lashe wannan gasar za ta zama wata karin damar haskakawa ga wannan dan wasan tsakiya da ba’a cika lura da kokarinsa ba.