Aluko ya tafi jinyar makonni 10

'Yan wasan Hull City zasu yi rashin Aluko
Image caption 'Yan wasan Hull City zasu yi rashin Aluko

Dan Najeriya Sone Aluko da ke buga wasa a kungiyar Hull City ya shiga jiyar makonni takwas zuwa 10 bayanda ya samu rauni a agararsa.

Aluko ya fice daga wasan da Hull ta yi nasara kan Sunderland 1-0 ranar Asabar bayanda ya koka da ciwon da ke kafarsa.

An sa ran dan wasan mai shekaru 24 zai dawo daga jiyyar raunin da ya samu a kafarsa bayanda ya kasa shiga wasannin da kungiyar ta kara da Tottenham a rukunin Premier da kuma kofin Capital One.

Aluko, wanda ya ci kwallo daya a bana, ya kwashe rabin karshe na kakar wasan bara ya na fama da jinyar kafa bayanda aka yi masa tiyata.