U17: Nigeria ta dauki kofi a karo na 4

Image caption Sau hudu kenan Nigeria na lashe wannan Kofi

Nigeria ta dauki Kofin Gasar kwallon kafa ta 'yan kasa da shekaru 17, wanda aka kammala a Hadaddiyar Daular Larabawa bayan ta doke Mexico da ci 3-0 a wasan karshe.

'Yan wasan Nigeria sun zira kwallaye daya tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, inda dan wasan Mexico Aguirre ya ci kansu.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci, sai Kelechi Iheanacho yaci kwallo na biyu a yayinda Musa Muhammed yaci kwallo ta uku.

Sweden ce ta zama ta uku a gasar bayan ta lallasa Argentina daci hudu da daya.

Karin bayani