'A PSG Ibrahimovic zai yi ritaya'

Image caption Zlatan Ibrahimovic

Shugaban kungiyar Paris St-Germain, Nasser Al-Khelaifi ya ce Zlatan Ibrahimovic zai ci gaba da buga kwallo har yayi ritaya.

Dan kwallon Sweden mai 32, ya koma PSG ne a bara, inda kuma ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar a watan Satumba har zuwa 2016.

Al-Khelaifi ya shaidawa BBC cewar " ya gaya mini a nan zai ci gaba da taka leda har yayi ritaya".

Ibrahimovic ne yafi kowanne dan wasa zira a gasar Faransa, inda yaci kwallaye 30 cikin wasanni 34 a kakar wasan da ta wuce.

Ya kuma taimakawa PSG ta lashe gasar Faransa a karon farko tun shekarar 1994.

Karin bayani