Silva zai yi jinyar makwanni 4

Image caption David Silva

Dan kwallon Manchester City David Silva zai yi jinyar makwanni hudu saboda raunin da yaji a tsakiyar mako.

Dan wasan Spain din ya samu raunin ne a wasan da City ta doke CSKA Moscow daci 5 da 2 a ranar Talata.

Bisa dukkan alamu, ba zai buga wasanni biyar ba a City amma watakila ya dawo wasa a ranar 7 ga watan Disamba.

Silva mai shekaru 27, ya zira kwallaye uku a kakar wasa ta bana a gasar Premier ta Ingila.

Sai dai kuma kocin Manchester City, Manuel Pellegrini na saran kyaftin din kungiyar Vincent Kompany zai komo wasa inda zasu hadu da Tottenham a ranar 24 ga watan Nuwamba.

Karin bayani