Al Ahly ta lashe kofin zakarun Afrika

Al Ahly of Egypt
Image caption Zakarun kofin Afrika a bana karo na Takwas

Kungiyar kwallon kafa ta Al Ahly ta lashe kofin zakarun Afrika, bayan data casa Orlando Pirates daci 2-0 a wasan da suka kara a filin wasa na Arab Contractors dake Alkahira.

Mohammed AbouTrika shi ne ya fara zura kwallo a minti na 54, sai da kuma aka kai minti na 78 ana gumurzu kafin Al Ahly ta kara kwallo ta biyu ta hannun Ahmad Abdel Zaer.

A fafatawar Farko da suka hadu a Soweto sun tashi 1-1,

Nasarar da Al Ahly ta samu yasa ta lashe kofin karo na takwas, kuma kungiyar zata wakilci Afrika a gasar cin kofin zakarun Duniya da Morocco zata karbi bakunci a watan Disamba.