Kofin zakarun CAF: Al Ahly ko Pirates

Al Ahly Pirates
Image caption Yau ne za a tantance zakaran kofin bana a Afrika

Mai rike da kofin zakarun Afrika Al Ahly za ta kara da Orlando Pirates a wasan karshe na cin kofin zakarun Afrika, bayan da suka tashi wasan farko 1-1 a satin da ya gabata.

An amince wa Al Ahly ta karbi bakuncin karawar da za su yi a yau Lahadi a filin wasanta na Arab Contractors dake Alkahira mai cin 'yan kallo 30,000, inda rabon da su yi wasa a filin tun watan Afrilu bisa fargabar rashin tsaro.

Al Ahly mai rike da kofin karo bakwai, tayi takaicin farke kwallo da akayi daf da atashi wasan da suka kara a Soweto, Ita kuwa Pirates na fatan ci gaba da saka kaimin lashe kofi a Alkahira.

Pirates daga Afrika ta kudu ta kai wasan karshe akan Esperance ta Tunisiya bayan da wasanni biyu da suka kara aka tashi wasa babu ci.