BT: Zai nuna wasannin zakarun Turai

Bayern Celebrates
Image caption Bayern Munich suna murnar lashe kofin bara

Kamfanin BT Sport ya bada sanarwar zai dauki damar nuna wasannin gasar cin kofin Zakarun Turai kai tsaye na tsawon shekaru uku a kan kudi kimanin Fan Miliyon 897.

Kamfanin ya sami izinin nuna wasanni 350 a kowacce kakar wasa tun daga shekara ta 2015, bayanda suka cimma yarje-jeniya da hukumar kwallon kafa ta Turai.

Jami'in hulda jama'a na BT ya ce "za mu girgiza kasuwar kallon wasanni a Birtaniya, do min za mu dinga nuna wasannin kofin zakarun Turai har da wasan karshe kuma a kyauta.

Cimma yarjejeniyar zai jawowa kamfanin Sky da ITV koma baya, domin a tsakaninsu suke raba daukar nauyin kawo gasar cin kofin zakarun Turai.