Ingila na fargabar raunin Gerrard

Steven Gerrard
Image caption Ingila na fatan raunin dan kwallon kar ya yi tsawo

Manajan Liverpool Brendan Rodgers ya ce Steven Gerrard zai sami sauki ya kuma halarci sansanin Ingila ranar Litinin, bayan da aka canja shi a karawar da suka yi da Fulham a raunin da ya dade dashi na kugu.

Kaftin din Ingila ya taimaka a wasan da Liverpool ta lashe da ci 4-0 a filinta na Anfield, amma aka canja shi a minti na 67.

Rodgers ya ce "har yanzu ban tattauna dashi ba, amma zai iya ajiye shi ya huta a wasan da ya kamata."

Satin da zamu shiga Ingila zata kara da Chile da Jarmus a wasannin sada Zumunci a Wembley, lokacin zai ragewa kocin Ingila Roy Hodson wasanni uku kafin ya fidda sunayen 'yan kwallon da zasu wakilci Ingila a gasar cin kofin duniya da Brazil wanda za ta dauki nauyi a shekara ta 2014.