Rooney: Za mu iya kare Kambunmu

Wayne Rooney
Image caption Mun dawo ganiyar wasaninmu domin kare kanbunmu

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney ya ce United za ta iya sake daukar kofin Premier fiye da Arsenal da za su karbi bakuncin ta a yau Lahadi.

United ta lashe kofin Premier da tazarar maki 11 a kakar bara, Arsenal ta tsere mata da tazarar maki takwas a bana kasancewar United ta fuskanci kwanciyar-hannu a farkon kakar banan.

Rooney ya ce "muna da tabbaci za mu lashe kofin Premier bana. Mun taba tsintar kanmu a irin wannan yanayin amma muka yunkuro muka lashe kofin, kuma mun dawo ganiyar wasanmu a yanzu."

Tun a baya Rooney mai shekaru 28, ya ce za a yi saurin yabo idan aka ce Arsenal za ta iya lashe kofin Premier, saboda ta saba da tabukawa a farkon kakar wasa daga baya ba za aji duriyarta ba.