Messi zai yi jinyar kusan makwanni 8

Lionel Messi
Image caption Dan kwallon yana fama da jinyar rauni a bana

Dan kwallon Barcelona Lionel Messi zai yi jinyar raunin da ya ji na tsawon sati shida zuwa takwas sakamakon tsagewar tsoka da ya gamu dashi a cinyarsa.

Dan kwallon mai shekaru 26, ya fadi a fili ranar Lahadi a wasan da suka doke Real Betis bisa dalilin yagewar tsoka a cinyarsa ta hagu.

Messi dan Argentina yana fama da jinyar rauni a kakar wasan bana, sai da ma aka canja shi a karawar da sukayi da Atletico Madrid a watan August sakamakon raunin da ya ji a cinyarsa ta dama.

A watan Satumba ma ya samu rauni a cinyarsa lokacin da suka kara da Almeria