Da wuya Arsenal ta ci Premier - Moyes

David Moyes na tababar nasarar Arsenal
Image caption David Moyes na tababar nasarar Arsenal

Kocin Manchester United David Moyes ya ce sai an kai ruwa rana kafin fitar da zakaran gasar Premier na bana bayanda kungiyarsa ta yi nasara kan Arsenal mai jagorar rukunin.

Nasarar 1-0 da United ta samu a Old Trafford ta rafe tazarar da ke tsakaninsu da Arsenal zuwa biyar, yayinda Chelsea, Manchester City da Tottenham suka yi asarar maki.

"Ba na tsammanin akwai wata kungiya da za ta iya fintinkau" in ji Moyes.

"Ina jin za'a yi ta dauki ba dadi. Bana kam ba za'a san zakara ba sai an gama."