An baiwa U 17 na Nigeriya kyautar kudade

Nigeria U17
Image caption Nigeriya ta lashe kofin karo hudu

Shugaban Nigeria, Dr Goodluck Jonathan, ya shirya liyafa irin ta alfarma ga 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar 'yan kasa da shekara 17 sakamakon cin Kofin Duniya da suka yi.

Shugaban kasar ya karrama 'yan wasan ne a fadarsa, tare da ba su tukwicin Naira Miliyon biyu kowannensu.

Matasan 'yan kasa da shekaru 17 sun lashe kofin duniya karo na hudu a ranar Juma'a, bayan da suka doke Mexico da ci 3-0 a Abu Dhabi.

Shugaban kasar ya sanar da bai wa kowanne dan wasa Naira Miliyan biyu, Miliyan uku da kuma miliyan biyu da rabi ga koci da mataimakansa.

Sauran jami'an tawagar an ba su kudi daga kan Naira 300,000 zuwa 500,000 kowannensu.

Goodluck ya yi alkawarin zai karramasu da lambobin girma na kasa, ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su mara masa baya da sakawa 'yan wasan.