Carrick da Welbeck ba za su buga wasan Ingila ba

Carrick Welbeck
Image caption Hukumar FA ta ce ba zata maye gurbin 'yan wasan ba.

'Yan kwallon Manchester United Michael Carrick da Danny Welbeck ba za su buga karawar da Ingila za ta yi da Chile da Jamus a wasan sada zumunci ba.

Carrick, dan wasan tsakiya mai shekaru 32, yana fama da ciwon agara, shi kuwa Welbeck mai shekaru 22 , yana fama da ciwon gwiwa.

Ingila za ta kara da Chile a wasan sada zumunci ranar Juma'a, sannan ta kara da Jamus ranar Talata mai zuwa a filin wasa na Wembley.

Carrick ya fara bugawa Ingila wasa a karawar da suka yi da Mexico a watan Mayu na shekarar 2001, ya kuma buga wasanni 31.

Shi kuwa Welbeck ya fara kwallo a karawar da Ingila ta yi da Ghana a watan Maris ya kuma zura kwallaye 20.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce ba za ta maye gurbin 'yan wasan ba.