Djokovic ya lallasa Nadal a Tennis

Gwarzon tennis Novak Djokovic
Image caption Gwarzon tennis Novak Djokovic

Novak Djokovic ya rike kambunsa na zakaran gasar tennis ta ATP World Tour Finals inda ya lallasa dan wasan tennis na daya a duniya Rafael Nadal.

Dan kasar Serbia, wanda a watan jiya Nadal ya sauka daga matsayi na day zuwa na biyu ya lashe wasan ne 6-3 da 6-4 a filin O2 da ke London.

Wasanni 22 ke nan a jere Djokovic mai shekaru 26 ya na samun nasara, yayinda ya lashe gasar ta karshen shekara a karo na uku.

Yanzu kuma zai nufi Belgrade ne inda Serbia za ta kara da Jamhuriyar Czech a wasan karshe na cin kofin Davis ranar Juma'a.