Makiyan United zasu ji kunya- Jones

Phil Jones
Image caption Dan kwallon ya ce sai sun kunyata masu son suga sun kasa

Mai tsaron baya na Manchester United Phil Jones ya ce makiyan kungiyar sun zaku su ga United ta kasa kai bante ganin bata fara kakar wasan bana da sa'a ba.

Masu rike da kofin Premier sun lashe wasanni uku daga cikin wasanni takwas a karkashin sabon koci David Moyes a kakar bana.

Sai dai nasarar da suka lashe Arsenal da ci daya mai ban haushi ya sa kungiyar ya rage tazarar maki biyar tsakaninta da Arsenal a matsayi na biyar a teburin Premier.

Jones mai shekaru 21 ya ce "Jama'a na son ganin mun gaza, saboda mun lashe kofuna karo da dama, kowa ya tsani kungiyar da tayi fice."

"Ita kenan maganar, kuma United ta lashe kofuna tun kafin na shigo kungiyar."