An sallami Vidic daga asibiti

Nemanja Vidic ya bugu a kansa.
Image caption Nemanja Vidic ya bugu a kansa.

An sallami kyaftin din Manchester United Nemanja Vidic daga asibiti bayan buguwar da ya samu a wasan Premier da suka doke Arsenal 1-0.

An musanya Vidic, mai shekaru 32 ne daf da tafiya hutun rabin lokaci bayanda ya yi karo da golan United David De Gea.

"An sallami Nemanja Vidic ne daga asibiti bayan da ya samu buguwar ka," in ji wata sanarwa da United ta fitar.

Ba dai a sa ran zai sake buga wasa sai ranar 24 ga Nuwamba lokacin da United za ta ziyarci Cardiff a wasan Premier.