Har yanzu ina kishirwar kofi

Arsene Wenger
Image caption Wenger ya kwace shekaru 18 yana horadda Arsenal

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce kishirwarsa ta lashe kowanne irin wasa da zai kara da kowacce kungiya ba ta yi kasa ba a tsawon shekaru 18 da ya yi yana horar da kungiyar.

Kocin mai shekaru 64 har yanzu bai amince da tsawaita kwantaraginsa da kungiyar ba, duk da kwantaraginsa za ta kare a kakar wasan badi.

Wenger ya sanar a shafin Twitter na kungiyar a shirin tambaya da amsoshi "Hakika ina da tararrabi a zuciyata, amma abinda yafi tsaya min shi ne kishirwar na lashe dukkan wasannin mu"

Arsenal tana matsayi na daya a teburin Premier da tazarar maki biyu.

Kodayake ta yi rashin nasara a hannun Manchester United ranar Lahadi, rabon da ta yi rashin nasara a wasa tun a wasan farko da aka bude kakar bana.