Brazil 2014: Babu wurin gwajin kwayoyi a kasar

Ana gwajin jini da bawalin 'yan wasa don tantance amfani da haramtattun kwayoyi.
Image caption Ana gwajin jini da bawalin 'yan wasa don tantance amfani da haramtattun kwayoyi.

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta ce za ta yi amfani da wata cibiyar gwaje-gwajen lafiya da ke Switzerland ne wurin gwajin amfani da haramtattun kwayoyi tsakanin 'yan wasan da za su shiga gasar cin kofin duniya ta Brazil 2014.

Brazil, mai masaukin baki ba ta da amintacciyar cibiyar gwajin amfani da haramtattun kwayoyin.

A farkon shekarar nan ne hukumar yaki da kwayoyin kara kuzari ga 'yan wasa ta duniya ta soke lasisin cibiyar da ke Rio de Janeiro.

Da yake ba za'a iya mayar da cibiyar lasisinta kafin lokacin fara gasar ba, Fifa ta yanke shawarar aike wa da jini da bawalin 'yan wasan zuwa Switzerland.

Ko a gasar zakarun nahiyoyi da aka gudanar ta bana da aka gudanar a Brazil, a wannan cibiyar ta Switzerland aka tantance 'yan wasan.