Gerrard da Kyle ba zasu buga wasan Ingila ba

Gerrard Kyle
Image caption 'Yan wasan biyu na fama da rauni

Kaftin din Ingila Steven Gerrard da mai tsaron baya Kyle Walker ba zasu buga karawar da Ingila za tayi da Chile a Wembly ba, sakamakon raunin da suka samu.

Dan wasan tsakiya Gerrard, mai shekaru 33 ya sami rauni a kugunsa a karawar da Liverpool ta lashe Fulham, yayin da shi kuwa Walker da ke yi wa Tottenham wasa bai halarci atisayen 'yan wasan Ingilan ba a yau Laraba.

Sai dai dan kwallon Chelsea mai wasan tsakiya Frank Lampard, da bai ji dadin jikinsa ba, ya fara atisaye tare da tawagar 'yan wasan.

Haka kuma Michael Carrick, mai shekaru 32, da Danny Welbeck sun fice daga tawagar ta Ingila.

Saboda 'yan wasan biyu na Manchester United, daya yana fama da ciwon agara daya kuma yana fama da ciwon gwiwa.

Bayan wasan Ingilan da Chile ba kuma za su yi wanda kasar tasu za ta yi da Jamus ba a ranar Talata.