A sa 'yan gida 3 a duk wasa - PFA

'Yan wasan Ingila na fargabar karancinsu a Premier zai yi illa ga kungiyar kasar
Image caption 'Yan wasan Ingila na fargabar karancinsu a Premier zai yi illa ga kungiyar kasar.

Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa na Ingila da Wales PFA za ta aike da wata shawara ga hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa, wacce zata bukaci tilastawa kungiyoyin kwallon kafa su rinka sa akalla 'yan wasa uku na gida cikin masu taka musu leda a matakin farko.

Kungiyar zata tattauna wannan batun ne daidai lokacin da ake fargabar cewa fam miliyan 897 da kamfanin BT Sport ya biya don nuna wasannin Turai a talabijin zai zama karin matsin lamba ga kociyoyi da su saka 'yan wasan da suka riga suka yi fice sabanin matasa.

Bangaren wasannin na BBC dai ya bada rahoton cewa adadin 'yan wasan Ingila 'yan kasa da shekaru 21 da ke buga wasa a rukunin Premier ya yi kasa sosai.

Dokokin Tarayyar Turai dai sun hana nuna wariyar 'yan kasanci a kowanne irin aiki, amma kungiyar ta PFA na ganin tunda matsalar ta shafi manyan rukunonin wasan kwallon kafa biyar na Turai, Uefa za ta iya daukar matakin ba tare da saba doka ba.