Roy ya sallamawa Afrika a Brazil 2014

Kocin Ingila Roy Hodgson
Image caption Kocin Ingila Roy Hodgson

Kocin Ingila Roy Hodgson ya ce: "Kungiyoyin Afrika sun fi na Turai damar lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a Brazil 2014."

Yayinda Ingila ta samu gurbin shiga gasar, kungiyoyin Afrika zasu buga wasanninsu na karshe na neman shiga gasar ne nan gaba a cikin watan nan.

Ko wadanne kungiyoyi biyar ne daga Afrika suka samu shiga, Hodgson na ganin za su fi samun dama saboda yanayin Brazil ya dace da na Afrika.

Ya kuma kara da cewa: "Su na da kwararrun 'yan wasa da suke bugawa a Turai musamman ma Nigeria."