Eto'o ya shawarci 'yan kwallon Kamaru

Samuel Eto'o
Image caption Eto'o na fatan 'yan Kamaru za su mara musu baya

Samuel Eto'o ya roki 'yan Kamaru da su tashi tsaye su hada kansu domin taimakawa kungiyar kwallon kafa ta kasar samun gurbin shiga gasar cin kafin duniya a badi.

Kamaru ta tashi wasa babu ci a karawar da tayi da Tunisia, tuni Eto'o ya ce a manta da rashin jituwar dake tsakaninsa da hukumar kwallon kafa ta kasar domin maida hankali a karawar da za suyi ranar Lahadi mai zuwa.

Eto'o ya ce "Ya kamata mu manta da bambamce-bambamcen dake tsakaninmu domin samun tikitin shiga kofin duniya".

Dan wasan ya yi zargin cewa abokan wasansa sun ki bashi kwallo a karawar farko, a inda ya kara da cewa yana da shaidar faifan bidiyo da zai tabbatar da zarginsa.

Dan wasan ya shaidawa kocin Kamaru Volker Finke, cewa baya fatan abinda ya faru ya sake faruwa a kungiyar, wanda tuni kocin ya manta da maganar abinda ya faru.