Manchester United ta ci riba

Manchester United
Image caption Kungiyar tana sa ran samun karin kudin shiga a bana

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ba da sanarwar cin riba ta kimanin fam Miliyan 99, bayan watanni uku na farkwan shekaran nan.

Kungiyar ta samu karin kaso 29 cikin dari bayan da ta samu karin daukar nauyinta da kuma kudin da take samu a nuna wasanninta da ya karu da kaso 63 daga cikin dari.

Haka kuma ta samu karin kamfanunnuka da suke daukar nauyinta har guda 12 ciki har da kamfanin zirga zirgar jiragen sama da ke Rasha wato Aeroflot.

Kungiyar ta yi hasashen za ta sami kudin shiga a bana da zai kai kimanin fam miliyan 420 zuwa 430, kuma hakan zai danganta ta da kungiyoyin da suka fi arziki a nahiyar Turai, wato Real Madrid da Barcelona.

Iyalan Glazer sune suke gudanar da kungiyar Manchester