WestBrom na son nazari kafin bada fenariti

An ba Chelsea fenariti bayan karon Reid da Ramires
Image caption An ba Chelsea fenariti bayan karon Reid da Ramires

West Brom ta bukaci a rinka duba hotunan bidiyo kafin bada bugun fenariti a rukunin Premier.

Kocin West Brom Steve Clarke ya fusata da fanaritin da aka baiwa Chelsea a karshen wasan da suka tashi 2-2 a makon jiya a filin Stamford Bridge.

A wasikar da ya aikawa hukumar Premier, shugaban kungiyar Jeremy Peace ya ce sau hudu ana baiwa abokan karawarsu a fenariti ba bisa ka'ida ba.

Baya ga wasan Chelsea - inda aka bada fenariti sanadiyyar karon Steven Reid da Ramires - West Brom ta ce an bada haramtacciyar fenariti a wasansu da Southampton, Arsenal da Stoke.

Kungiyar ta ce ba don wadannan fenaritin ba da yanzu ta na da karin maki bakwai kuma a matsayi na biyar a Premier sabanin 10 da take kai yanzu.