Dole Ingila ta yi rawar gani a 2014 - Klinsmann

Jurgen Klinsmann
Image caption Klinsmann ya kalubalanci Ingila

Gwarzon dan kwallon Jamus Jurgen Klinsmann ya ce wajibi ne Ingila ta kai matakin takwas na karshe a gasar cin kofin duniya ta 2014 idan ta na son rike kambunta na "cibiyar kwallon kafa."

Klinsmann, wanda yanzu shi ne kocin Amurka ya yi shekaru biyu yana buga wasa a kungiyar Tottenham.

Ya ce: "Ingila na cikin manyan kasashen kwallon kafa amma dole ne ta tabbatar da hakan ta hanyar isa matakin daf da na kusa da na karshe."

Amurka, wacce ta samu shiga gasar karkashin jagorancin kocin mai shekaru 49, za ta buga wasan sada zumunci da Scotland ranar Juma'a.

Klinsmann ya bugawa kasarsa wasa sau 108 kuma ya na cikin kungiyar Jamus ta Yamma da ta doke Ingila a wasan kusa da na karshe a 1990 kafin su lashe kofin dungurungum.