Sharhi Kai Tsaye a kan wasan Nigeria da Ethiopia

Nigeria na fafatawa da Ethiopia a filin wasa na U.J Esuene dake birnin Calabar a yau Asabar.

Latsa nan don sabunta shafin

1830: Mun gode da karanta wannan sharhi a kan wasan Nigeria da Ethiopia wanda aka tashi 2 da 0 a filin Calabar wato kenan Nigeria ta ci 4 Ethioia kuma 1 a bugu biyu. Sai mun hadu a Brazil a shekara ta 2014.

18:21: A ranar 6 ga watan Disamba ne za a rarraba yadda kasashe za su fafata da junansu a zagayen farko na gasar cin kofin duniya na Brazil.

18:17: Dan kwallon Nigeria Ogenyi Onazi ya shaidawa BBC cewar "Wannan shi ne abinda yafi min dadi a rayuwata, gasar kofin duniya ita ce abinda tafi komai a kwallon kafa."

18:12: Kamar yadda ya faru a shekarar 1994, a bana ma Nigeria ta tsallake zuwa gasar kofin duniya a matsayinta na zakaran kwallon Afrika. Sai dai a 1994, Italiya ce ta yi wa Nigeria cikas a zagaye na biyu. Shin za a samu sauyi a Brazil a shekara ta 2014.

18:10: Ra'ayoyi:

twitter@bbchausa: "Gabadai gabadai Super Eagles, kun yi rawar gani, kuma ga dukkan alamu za mu bai wa maza kashi a Brazil."@Bshrzaria

"Ya yi kyau, Najeriya ta lashe Habasha a kwallon kafa" @abubakar47i

18:06: Magoya bayan Super Eagles, shin mai Stephen Keshi zai iya yi a Brazil 2014? Yaya kuka ga kamun ludayinsa kawo yanzu? Aiko da ra'ayoyinku a BBC hausa facebook ko a twitter@bbchausa ko email hausa@bbc.co.uk ko kuma sakon waya 0044778620202009

18:04: Ra'ayoyi

BBC Hausa Facebook: "Da kyar na sha yafi da kyar aka kamani. Ina taya 'yan wasan Nigeria murna da fatan zasu taka rawar gani a gasar kofin duniya. Up Super Eagles." Mudasser Sani Birnin Kebbi

18:00: Karfe 8 agogon Nigeria, kallo zai koma birnin Dakar, inda Senegal za ta dauki bakuncin Ivory Coast. A wasan farko Ivory Coast ta doke Senegal daci 3 da 1.

17:57: Shekara ta 2013 ta zo wa Nigeria da kafar dama a fagen kwallon kafa. Super Eagles ta lashe gasar kofin Afrika, sai Golden Eagles ta lashe gasar kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 17. Sannan kuma ga tsallakewa zuwa gasar kofin duniya na badi.

17:55: Ra'ayoyi:

00447786202009: "UP UP UP NAJERIYA." ABBA SULAIMAN GOGORI

17:52: An tashi wasa Nigeria 2-0 Ethiopia.

17:51: An shiga mintunan karin lokaci. Tabbas Nigeria za ta je gasar Brazil 2014 saboda Ethiopia bata da isasshen lokacin farkewa.

17:43: Ra'ayoyi:

00447786202009: "Ja mu je zakarun kwallon Africa watau Nigeria. Allah ba mu sa'a da nasarar karawa. Up Nigeria!" Muhd Ahmad Idris Kabuga Kano

BBC Hausa Facebook: "Wasa yana tafiya yadda nake so, tunda mu ke kan gaba." Muhammad Salees

17:39: Nsofor ya ci kwallo. Nigeria 2-0 Ethiopia

17:30 Bargicho na Ethiopia ya samu yalo kati bayanda ya kada Emenike na Nigeria

17:36: Obinna Nsofor ya canji Victor Moses a bangaren Nigeria

17:33: An fara ruwan sama a filin wasa na U.J Esuene dake Calabar

17:32: Hinisa ya canji Bekele a bangaren Ethiopia

17:28: Har yanzu wasa Nigeria 1-0 Ethiopia. Idan an tashi haka Nigeria za ta samu shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya

17:26: Salahaddin Sa'id na Ethiopia ya samu yalo kati bayan da ya fadi da niyyar neman fenariti daf da ragar Nigeria

17:25: Azubuike na Nigeria ya shigo a madadin Emeruo

17:24: Ra'ayoyi

Twitter@bbchausa: "Duk da kwallon da nigeria ta ci, 'yan wasan ba sa buga mana wasa mai kyau."@rabiumaharazukt

17:21: Ethiopia ta samu bugun tazara daf da ragar Nigeria

17:20: Ahmed Musa na Nigeria ya kai hari ragar Ethiopia sai dai alkalin wasa yace ya yi satar gida.

17:18: Assefa ya canji Kebede a bangaren Ethiopia

17:15: Sunday Mbah na Nigeria ya shigo a madadin Ideye

17:14: An fitar da Nigeria Ogbuabuna daga filin kwallo bayan da ya samu rauni

17:11: Bekele na Ethiopia ya kai hari ragar Nigeria, gola Enyeama ya kama kwallo

17:10: Kyaftin din Ethiopia ya kayar da Mikel Obi na Nigeria, abinda ya jawo masa yalo kati

17:09: 'Yan wasan Ethiopia sun kai kora ragar Nigeria amma ba nasara

17:03: An dawo daga hutun rabin lokaci

16:47: An bai wa dan Nigeria Kenneth Emeruo yalo kati bayand ya kayar da Sa'id na Ethiopia.

16:47: An busa hutun rabin lokaci. Nigeria 1-0 Ethiopia.

16:46: Ethiopia ta samu bugun tazara amma golan Nigeria Enyeama ya buge ta

16:45: An bada karin mintu biyu a rabin lokaci na farko

16:39: Ra'ayoyi:

BBC Hausa Facebook: "Mu je zuwa Naija." Ahmad Sani Mai Wake. "Gaba dai gaba dai Nigeria ku casa mana su." Abdurrahman Isma'il Guruza.

16:36: Ethiopia ta barar da bugun tazara

16:34: Ethiopia ta buga kwana amma golan Nigeria Enyeama ya rike kwallo

16:32: Yanzu haka dai Nigeria na gaban Ethiopia daci 3 da 1 bayan bugu gida da waje

16:30: Ideye na Nigeria ya kara wani harin amma kwallon ta bugi karfen raga ta yi waje

16:29: Ahmed Musa na Nigeria ya kai hari amma kwallo ta fice

16:29: Golan Nigeria Enyeama ya kade bugun tazara daga Ethiopia.

16:25: Ehiopia ta buga kwana amma ba ta samu nasara ba

16:22: Ra'ayoyi:

BBC Hausa Facebook: "Hahahaha dama na fada ruwa ba sa'an kwando bane up nigeria" Muhammad Babangida Rijiyar Lemo

"Yayi kyau da muka sha su." Bala Bitrus

Image caption Victor Moses yaci da fenariti

16:19: Goal! Nigeria 1-0 Ethiopia. Victor Moses ne ya buga

16:18: Aynalam Hailu ya taba kwallo da hannu an ba Nigeria fenariti

16:15: Nigeria ta doka bugun tazara sai dai golan Ethiopia ya kade

16:14: Dan wasan Ethiopia Aynalam Hailu ya kada Emenike na Nigeria

16:12: Dan wasan Ethiopia Salahadin Sa'id ya kai hari ragar Nigeria amma bai yi nasara ba.

16:10: Ethiopia na kokarin zama kasar farko daga yankin gabashin Afrika da za ta tsallake zuwa gasar cin kofin duniya.

16:10: Nigeria na neman zuwa gasar kofin duniya a karo na biyar. Bayan an fafata tare da ita a shekarar 1994 da 1998 da 2002 da kuma 2010.

16:06: Nigeria sanye da koriyar riga da gajeren wando kore a yayinda Ethiopia ke sanye da ruwan kwai sama da kasa

16:02: Super Eagles ta kai harin farko sai dai kwallo ta fita

16:00 An fara taka leda Ethiopia ce da bugun farko

15:57: An buga taken Nigeria a filin wasa na U J Esuene dake Calabar a shirin fara wasa

15:56: sauran minti hudu a soma taka leda a Calabar. Shin wane dan kwallo ne zai soma zira kwallo? Aiko mana da ra'ayoyinku ta email hausa@bbc.co.uk ko a BBChausa Facebook ko ta 00447786202009

15:52: TAURARIN 'YAN WASA:

Dan kwallon Nigeria, Emmanuel Emenike shi ne watakila zai kasance zakara a wasan. Ya zira kwallaye biyu a karawar farko. Shin ko wacce irin rawa zai taka a yau?

Dan wasan Ethiopia Getaneh Kebede zai buga wasan. Shi ne zakara a bangaren Ethiopia kuma bai buga wasan farko ba. Shin dawowarsa wasa za ta karawa Ethiopia kwarin gwiwa?

Ra'ayoyi:

15:47: FIFA.com: "Ethiopia za ta doke Nigeria daci 3 da 2" in ji Mebrish dan Ethiopia.

15:39: Alkalin wasa: Bakary PAPA GASSAMA

Image caption Magoya bayan Super Eagles ta Nigeria

Ethiopia: Sisay BANCHA (Gola), Alula GIRMA, Getaneh GIBETO, Butako ABEBAW, Aynalem HAILU,Salahdin AHMED Asrat GOBENA, Bargicho SALAHADIN, Minyahile BEYENE, Shemeles BEKELE, Girma ADANE. Koci: Sewenet BISHAW

Image caption 'Yan wasan Super Eagles, Nigeria

15:34: 'Yan wasan da za a soma dasu:

Nigeria :Vincent ENYEAMA (Gola), John Obi MIKEL, Kenneth OMERUO, Godfrey OBOABONA,Uwa ECHIEJILE,Efe AMBROSE, Ahmed MUSA,Brown IDEYE, Emmanuel EMENIKE, Victor MOSES, Ogenyi ONAZI. Koci: Stephen Keshi

15:28: Sauran kasashen Afrika dake kan hanyarsu ta zuwa Brazil sune Ghana, Cameroon, Tunisia, Ivory Coast da kuma Burkina Faso.

Ra'ayoyi:

Twitter@bbchausa: "Hakika tarihi ne zai maimaita kansa #Ethiopia sai ku rungumi kaddara domin ba sani ba sabo.Up Super Eagles." @abba_geidam

15:25: A karawar farko tsakaninsu a Addis Ababa, Nigeria ta doke Ethiopia daci 2 da 1. Emmanuel Emenike ne yaci kwallayen biyu.

Ra'ayoyi:

BBC Hausa Facebook: "Dama Hausawa na cewa ko ba'a gwada ba, linzami yafi karfin kaza. Ba shakka muna da Alamun Nasara a wannan wasan da Ethiopia." daga Aminu Dankaduna Amanawa.

Image caption Magoya bayan Waliya Antelopes ta Ethiopia

15: 17: Nigeria ta yi nasara a wasanni shida, Ethiopia ta yi nasara a wasa daya yayinda suka yi canjaras sau daya. Ko wace kasa ce za ta yi nasara a wannan karon?

15:09: A tarihi Ethiopia da Nigeria sun kara sau takwas

15:02: Ga ra'ayoyin wasu daga cikin masu bibiyar shafinmu na BBC Hausa a Facebook.

Image caption 'Yan wasan Waliya Anetelopes, Ethiopia

Aliyu Muhammed: "Ai 'yan Ehiopia za su san fada da aljani ba riba, dan za su kwashi kashinsu a hannu yau a wurin Super Eagles."

Mohammed Shuwa: "Ai mu 'yan Nigeria mun riga mun wuce, sai dai muce Allah yasa a samu a rukuni mai sauki."

Abdulultimate Muhammed: "Nigeria 5-0 in Allah ya yarda."

15:00: Barkanmu da saduwa cikin wannan shiri na musamman inda za mu kawo muku bayanai kai tsaye ta wayar salula game da wasan nema shiga gasar cin kofin duniya tsakanin Nigeria da Ethiopia.

Nigeria dai ta yi nasara kan Ethiopia da ci 2-1 a karonsu na farko.

Karin bayani