Nigeria za ta buga gasar kofin duniya

Image caption 'Yan wasan Super Eagles

Zakarun kwallon Afrika, Nigeria ta kasance kasa ta farko a nahiyar da ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil, bayan ta doke Ethiopia daci 2 da 0 a ranar Asabar.

Victor Moses da Obinna Nsofor sune suka ci wa Super Eagles kwalayenta biyu, kuma sakamakon ya nuna cewar an tashi 4 da 1 a bugu biyu tsakanin kasashen biyu.

Moses ya ci kwallonsa a bugun fenariti bayan dan Ethiopia Aynalem Hailu ya taba kwallo da hannu a cikin da'ira na 18, sai kuma Nsofor yaci ta biyu ana sauran mintuna 8 a tashi wasan.

Kenan Nigeria ta tsallake zuwa gasar cin kofin duniya sau biyar kenan.

Karin bayani