FIFA: Zaben Burundi ya yi kyau

Image caption Anyi zaben shugaban Hukumar kwallon kafa a Burundi

Hukumar Kwallon kafa ta Burundi ta sami sabon zababben shugaba Reverien Ndikuriyo wanda ya maye gurbin Lydia Nsekera.

Reverien ya zama shugaba ne bayan zaben da akayi wanda Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta bayyana shi a matsayin ingantaccen zabe.

Lydia Nsekera dai ita ce mace kwaya daya tilo shugabar Hukumar kwallon kafa ta kasa in banda shekarar da ta gabata.

Sai dai Nsekeran za ta ci gaba da kasancewa a kwamitin zartarwa na FIFA.

Karin bayani