Za mu nuna wa Jamus iyawa - Gerrard

Steven Gerrard
Image caption Gerrard zai kamo tarihin kyaftin din Ingila Bobby Moore na buga wasanni 108 yau.

Kyaftin din Ingila Steven Gerrad ya ce kasarsa za ta nuna wa Jamus cewa fa sun bunkasa a wasansu ranar Talatar nan.

Kasashen biyu za su kara ne a wasan sada zumunta a Wembley.

Rabonsu da haduwa tun a gasar Kofin Duniya zagayen 'yan 16 a 2010 a Afrika ta Kudu inda Jamus ta casa Ingila 4-1.

Gerrad ya ce, ''ba na jin cewa idan za mu hadu da Jamus a gasar Kofin Duniya gobe za su ci mu 4-1.''

Dan wasan na Liverpool, mai shekaru 33, ya ce yana jin cewa yanzu sun fi karfi sosai saboda suna da 'yan wasa matasa da kwararru wadanda ke bunkasa ko da yaushe.

Idan Ingila ta yi rashin nasara a wasan hakan zai zama cewa ta yi rashin nasara sau biyu a jere a Wembley karon farko a shekaru 36, saboda Chile ta ci su ranar Juma'a 2-0.