Ghana za ta je gasar Kofin Duniya

'yan wasan Ghana
Image caption Karo na uku a jere ke nan Ghana za ta gasar Kofin Duniya

Ghana ta sami damar shiga gasar kwallon kafa ta Kofin Duniya da za a yi a Brazil a 2014.

'yan wasan Ghanan na Black Stars sun sami damar ne a karshen wasansu da Masar bayan an tashi Masar din ta ci 2-1.

Masar din ta kasa fanshe ci 6-1 da Ghana ta yi mata a karawarsu ta farko da suka yi a Kumasi.

Jumulla sakamakon yanzu ya kasance Ghana tana da ci 7 Masar kuma na da 3 wasa gida da waje.

Ghana ta bi sahun Najeriya da Ivory Coast da Kamaru wajen samun gurbi biyar na Afrika a gasar ta Duniya.

Idan an jima ne za a yi wasan neman gurbi na biyar na karshe da ya rage tsakanin Burkina Faso da Algeria.

Karin bayani