An kashe makiyaya uku a Plateau

kasuwar shanu a Najeria
Image caption Matsalar sace wa fulani makiyaya shanu a Plateau ta ki ci ta ki cinyewa

An kashe makiyaya akalla uku, aka kuma jikkata daya a jihar Filato a Nijeriya.

An kuma sace shanun makiyayan fiye da dari a karamar hukumar Barkin Ladi ta Filaton.

Biyu daga cikin Fulani makiyayan dai an ce 'yan bindiga ne suka kwace su daga hannun jami'an tsaro suka kashe su nan take.

Yayin da suke yi wa jami'an tsaron rakiya domin karbo masu shanun nasu daga hannun barayin masu dauke da makamai.