Qatar 2022: walwalar ma'aikata za ta karu

Image caption Ma'aikata 'yan ci rani za su sami walwala a Qatar

Hukumar dake kula da tsara gasar cin kofin duniya da za ayi a Qatar a 2022 ta ce ta yi tattaunawa mai ma'ana da Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International.

Kungiyar Amnesty Iternational dai ta zargi Kamfanonin gine-gine da musgunawa ma'aikata 'yan ci rani a kasar.

Kwamitin koli na Qatar 2022 ya ce zai fitar da sanarwar tsare-tsare na walwala ga ma'aikatan a karshen wannan shekarar.

Kuma a cewar Hukumomin Qatar din suna martaba gudunmawar Amnesty International.

Karin bayani