Sweden da Portugal za su yi karambatta

Image caption Za a yi fafata a wasan Sweden da Portugal

Dan tsakiyar kasar Sweden din nan Sebastian Larsson ya yi amannar cewa Alkalin wasa dan kasar Ingila Howard Webb ba zai fada tarkon Portugal ba yayin da kasashen biyu su ka hadu a wasa na biyu na fitowa gasar cin kofin duniya.

Alkalin wasa Webb shine zai jagoranci alkalancin wasan da za ayi a yau Talata a Solna; sai dai a wasan farko Portugal ta ci Sweden 1-0 a ranar Juma'a.

Larsson ya ce Howard Webb alkalin wasa ne na gaske wanda hakan na da mahimmanci ga wannan wasan mai girma.

Cristiano Ronaldo ne ya zuwa kwallo a kusan karshen wasan a wasan farko.

Karin bayani