Afrika na azamar hobbasa a gasar 2014

Image caption kasashen Afrika na yukurin cin kofin duniya

A Afrika kasashen da suka wakilci nahiyar a gasar kwallon kafa ta duniya 2010 su ne dai za su sake komawa wannan karon 2014.

Sai dai wannan karon ana fatan gogewar su za ta sa su kara gaba a inda yawanci ake waje da su.

Ana hasashen dai daya daga cikin Kasashen na Afrika zai hobbasa ya haura matakin wasan dab da na kusa da na karshe da suka je sau uku kuma basu haura matakin ba tun 1990.

Gogaggen dan wasannan Kyaftin din kasar Ivory Coast Didier Drogba ya ce wannan karon suna so su taka wata rawa daban sabanin shekarun baya.

Karin bayani