Kociya Gordon ya jinjinawa Bafana Bafana

Image caption Bafana bafana sun sami yabon kociyansu

Kociyan kasar Afrika ta kudu Gordon Igesund ya jinjinawa kokarin da 'yan tawagarsa suka yi kan cin Spain daya mai ban haushi a wasan sada zumunta da aka yi a Johannesburg ranar Talata.

Kwallon da dan gaban nan Bernard Parker ya zura a ragar Spain din a mintuna 56 ya jawo nasara akan zakarun duniya da kuma nahiyar Turai.

Kociyan Igesund ya yi mannar cewa Kungiyar kwallon kafa ta Bafana Bafana wadanda suka gaza fitowa gasar cin kofin duniya na kara inganta.

Nasarar da Afrika ta kudu ta samu ya karawa kungiyar kwallon kafar ta Bafana Bafana kwarin gwiwar tunkarar wasanni na gaba.

Karin bayani