Algeria ta cike gurbin Kofin Duniya

magoya bayan Algeria
Image caption Algeria ta yi sa'a ba ta ci kanta da kanta ba a kusan karshen wasan

Algeria ta zama kasa ta karshe da ta cike gurbin kasashen Afrika guda biyar na gasar Kofin Duniya ta kwallon kafa ta 2014.

Algeria ta yi nasara a kan Burkina Faso da ci 1-0 a karawar da suka yi ta biyu Talatar nan a birnin Blida na Algeria.

A wasansu na farko a watan da ya wuce Burkina Faso ta ci su 3-2.

Da sakamakon karawar ta biyu ya zama 3-3 sai dai Algeria ta yi nasara saboda kwallaye biyu da ta sanya a gidan Burkina Faso.

Karo na hudu ke nan Algeria za ta je gasar ta duniya kuma ta biyu a jere.

Kasashen da za su wakilici Afrika a gasar ta Duniya da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa su ne: Algeria da Kamaru da Ghana da Ivory Coast da Najeria.