2014: Wadanne kasashe ne za su Brazil ?

Image caption Magoya bayan Brazil

An samu karin kasashen da za su halarci gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil a shekara ta 2014.

A daren ranar Talata ne Ghana da Algeria da Faransa da Portugal suka tsallake bayan sun yi galaba a kan abokan karawarsu.

Afrika: Algeria da Kamaru da Ghana da Ivory Coast da Nigeria.

Asiya: Australia da Iran da Japan da Koriya ta Kudu.

Turai: Belgium da Bosnia-Hercegovina da Croatia da Ingila da Faransa da Jamus da Girka da Italiya da Spain da Netherlands da Portugal da Rasha da Switzerland.

Amurka ta Arewa da tsakiya: Costa Rica da Honduras da Amurka da Mexico.

Latin Amurka: Argentina da Brazil (Mai masaukin baki) da Colombia da Ecuador da Chile.

Karin bayani