Birmingham ka iya fitowa wasan kusa da karshe

Image caption 'Yan wasan Birmingham mata na kokari a gasar zakaru

Kungiyar kwallon kafa ta Ingila ta mata za ta kai ga wasan kusa da karshe na gasar zakaru ta mata bayan da Birmingham tayi kunnen doki da Arsenal a wasan dab da na kusa da karshe.

Birmingham za ta sami wata dama saboda wasan za ayi agidanta a zagaye na farko ranar 22 da 23 na watan Maris inda kuma za a yi wasan zagaye na biyu a Arsenal mako na gaba.

Arsenal dai ta kai ga wasan gab da na kusa da karshe da fifikon kwallaye 6-2 a kan Glasgow City, ita kuwa Birmingham ta doke kulob din Rasha ne na FK Zorkiy Kranogorsk.

Wadanda suka sami nasara kuma za su kara da Tyreos FF na kasar Sweden da kuma SV Neulenbach na Austria.

Karin bayani